NLC: Wajibi ne gwamnati ta fara biyan kananan ma'aikata N30,000 kafin zaben 2019
LABARAI DAGA 24BLOG
Waheed Olojede, shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Oyo, ya tabbatarwa ma'aikata cewa biyan N30,000 a matsayin albashi mafi karanci zai soma ne kafin babban zabe na 2019.
Olojede ya bayyana hakan a ranar Talata a garin Ibadan a bukin ranar 'yan fansho ta 2018 wanda 'yan fansho suka shirya a jihar.
Ya ce kungiyar ba zata ja baya akan ganin lallai gwamnatin tarayya ta biya N30,000 a matsayin albashi mafi karanci ga ma'aikatan kasar ba kafin nan da zuwan zaben 2019.
Olojede ya kuma bukaci shuwagabannin Nigeria da su sani cewa ma damar babu jama'a, to kuwa babu shugabanci don haka ya shawarce su akan yin tunani na kawo karshen wahalhalun da ma'aikata ke sha a kasar na rashin albashi mai tsoka da zasu rika kaiwa gida.
Haka zalika shugaban NLC na jihar, ya baiwa gwanatin jihar wa'adin kwanaki bakwai, da ta biya malaman makarantun firame albashinsu na watan Oktoba.
Olojede ya ce kungiyar ba zata ji shakkun daukar mataki ba ma damar gwamnatin jihar ta gaza cimma bukatarta na biyan malaman kudadensu kafin wa'adin kwanaki bakwai da kungiyar ta debar mata.
No comments:
Post a Comment