- LABARAI DAGA 24BLOG
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewar akwai ma su shiryawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, tuggu.
Osinbajo na wadannan kalamai ne a yau, Talata, yayin yayin taro da kwamitin tuntuba na jam'iyyar APC a birnin tarayya, Abuja.
Mataimakin shugaban kasar ya ce ma su shiryawa Buhari tuggu sun matukar girgiza bayan ya dawo cikin koshin lafiya daga zaman jinyar da ya yi a kasar Ingila.
A cewar Osinbajo, "dukkan ma su shirya tuggu sun taru a kan mutum daya da ake kira Muhammadu Buhari, kuma suna nan a ko ina - cikin 'yan siyasa, 'yan kasuwa, cikin malaman addini, da ma ko ina.
"Sun so ya mutu, amma sai ya dawo da karfinsa bayan koshin lafiya da ya samu," a kalaman Osinbajo.
Sannan ya kara da cewar daga cikin wadanda ke sukar shirin gwamnatin tarayya na tallafawa kananan 'yan kasuwa akwai shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki.
A cewar Osinbajo, "shirin mu na tallafawa kananan 'yan kasuwa (Trader Moni) na matukar bata ma su rai."
"Kullum cikin jin haushin wannan shirin tallafi su ke, amma mun san mugu ne kawai ke jin haushi saboda an taimaki talaka.
"Da amincewar majalisa mu ke gudanar da shirin tallafin.
"Tsari ne mai matukar muhimmanci ga gwamnatin mu, domin burinmu ne mu taimakawa kananan 'yan kasuwa.
"Wannnan shiri na bayar da tallafi na daga cikin dalilan wasu 'yan boko marasa kishin talaka na kullawa Buhari tuggu domin bata ma sa suna.
"Ku ma da kan ku za ku iya ganin cewar akwai ma su kullawa Buhari tuggu daga cikin manyan kasar nan."