Mun samu cewa, Mista Stanley ya bayar da wa'adin kwanaki 2 ga jam'iyyar kan gaggauta watsar da Atiku a matsayin dan takarar ta tare da yin kira kan aiwatar da wani sabon zaben fidda gwanin takara na jam'iyyar.
Osifo ya kuma yi barazanar gurfanar da jam'iyyar sa gaban Kuliya muddin ta gaza wajen tabbatar da wannan bukata da ya gindaya ta watsar da Atiku a matsayin gwanin ta na takara da kuma kiransa sake gudanar da sabon zaben fidda gwani.
Yayin ganawarsa da manema labarai cikin birnin Legas, Osifo ya bayyana cewa, dukkanin manema tikitin takara na jam'iyyar na cikakken alhaki na samun dama tamkar ta Atiku da a cewar sa kowanen su ya mallaki takardun neman kudirin takara daidai da na Atiku.
Dan takarar da ya kasance haifaffen jihar Edo ya bayyana cewa, takaicin sa ya takaita ne kadai dangane da ya yadda ya zubawa Sarautar Mai Duka idanu wajen halarta tare da shiga cikin sahun tantance manema tikitin takara da jam'iyyar ta gudanar yayin zaben ta na fidda na gwani.
Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, jam'iyyar ta PDP ta gudanar da zaben ta na fidda gwanayen takarar cikin farfajiyar wasanni ta Adokiye Amiesimaka da ke birnin Fatakwal na jihar Rivers a raar 6 ga watan Oktoba da ya gabace mu.