Full width home advertisement

Travel the world

Climb the mountains

Post Page Advertisement [Top]

'Yan sanda a Amurka na neman kwayoyin halittar Cristiano Ronaldo

'Yan sanda a birnin Las Vegas na Amurka sun bukaci a ba su kwayoyyin halittar DNA na shahararren dan wasan kwallon kafar nan, Cristiano Ronaldo, domin gudanar da bincike a kan zargin da ake yi masa na aikata fyade.
Lauyan dan kwallon Peter S. Christiansen ya shaida wa BBC cewa bukatar kawo kwayoyyin hallita ba sabon abu ba ne.
Jaridar Wall Street Journal ta wallafa cewa an aika takardar bukatar hakan ne zuwa wata kotu da ke kasar Italy.
Sai dai Ronaldo ya musanta zargin da ake masa na cin zarafin Kathryn Mayorga a wani otel da ke Las Vegas a 2009.
Tsamar Messi da Ronaldo ba ta kare ba
Ronaldo ya kalubalanci Messi ya same shi a Seria A
Cristiano Ronaldo ya yi watsi da zargin yin fyade
Lauyan dan kwallon ya bayyana cewa "Har yanzu Ronaldo yana kan bakarsa, abin da ya faru a Las Vegas a 2009, ba fyade ba ne, da amincewar ta, ba abin mamaki ba ne idan an ga kwayoyin halittar Ronaldo ko kuma 'yan sanda su nemi kwayoyyin domin bincike.''
Mujallar Der Spiegel ta kasar Jamus ce ta fara wallafa zargin da Ms Mayorga ta yi, bayan ta kai kararsa wajen 'yan sanda a Las Vegas bayan faruwar lamarin.
Mujallar ta bayyana cewa a shekarar 2010, Ms Mayorga ta yi wata yarjejeniyar sirri da Ronaldo a kan ya biyata dala 375,000 domin kada ta tona masa asiri.
Lauyan Ronaldo dai a baya ya bayyana cewa wanda yake karewa bai musanta yin wannan yarjejeinyar sirrin ba.
Ya kara bayyana cewa "wannan yarjejeniyar ba wai tana nuni da Ronaldo ya aikata abin da ake zarginsa da shi ba ne."
Lauyan Ms Mayorga ya bayyana cewa wata kungiya ta #Metoo Movement ce ta jawo ra'ayin Ms Mayorga da ta fito ta bayyana abin da ya faru, inda yanzu haka ta yi karar Ronaldo a Amurka.
Ronaldo dai ya koma kungiyar Juventus daga Real Madrid a kan fam miliyan 99.2.
Kuma ya ci kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Ballon d'Or a 2008, 2013, 2014, 2016 da kuma 2017.

No comments:

Post a Comment

Bottom Ad [Post Page]

| Designed by Colorlib | Distributed By Best BlogSpot Templates