Full width home advertisement

Travel the world

Climb the mountains

Post Page Advertisement [Top]

Wai jarumin Kannywood Sani S.K. ya rasu?

Fitaccen tauraron fina-finan Kannywood Sani Garba SK. ya musanta labarin da ke cewa Allah ya yi masa rasuwa.
A ranar Litinin ne wasu mutane da ke amfani da shafukan sada zumunta suka yi ta baza labaran karya a kan cewa ya rasu bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya.
Da ma dai tauraron na fama da rashin lafiya.
A hirarsa da BBC, sani S.K ya ce yana nan da ransa kuma yana samun sauki.
Ya bayyana cewa har ya gaji da amsa wayar tarho domin irin yawan mutanen da suke kiransa domin su ji ta bakinsa a kan ko da gaske ya mutu.
Amma dai tauraron ya ce yana fama da ciwon suga kuma ya gano hakan ne cikin 'yan kwanakin nan da ya je asibiti.
A baya dai an yada labaran karya a kan mutuwar wasu fitattun taurarin Kannywood, ciki har da Sadiya Gyale da Sani Moda.
An rika yada labarin mutuwar jarumi Sani S.K a Facebook.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment

Bottom Ad [Post Page]

| Designed by Colorlib | Distributed By Best BlogSpot Templates