Full width home advertisement

Travel the world

Climb the mountains

Post Page Advertisement [Top]

De Gea ya cire wa Manchester United kitse a wuta

Mai horar da Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya jinjina wa mai tsaren ragarsu, David De Gea bisa gagarumar rawar da ya taka a nasarar da suka samu kan Tottenham a gasar firmiyar Ingila, in da suka tashi 1-0.
Solskjaer da ke zama kocin rikon kwarya a kungiyar ya bayyana, De Gea a matsayin gola mafi kwarewa a duk fadin duniya, yayin da ya ce, golan na kokarin kafa tarihin da za a ci gaba da tunawa da shi a Manchester United.
Mai tsaren ragar ya kauwar da kwallayen da dama da Tottenham ta kai hare-harensu musamman bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Marcus Rashford ne ya jefa kwallon daya tilo a fafatawar ta ranar Lahadi.
Gabanin Solskjaer ya karbi aikin horar da Manchester Unted, akwai tazarar maki 8 tsakaninta da Arsenal, amma a yanzu kungiyar ta kulle wannan tazarar, in da kowacce daga cikinsu ke da maki 41.
Kocin ya samu nasara a dukkanin wasanni shida da ya jagoranci kungiyar tun bayan maye gurbin Jose Mourinho a cikin watan Disamba.
Ita ma Everton ta samu nasara akan Bournmouth da ci 2-0 a karawar da suka yi a gasar ta firimiyar Ingila, abin da ya ba ta damar darawa mataki na 10 a teburi.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment

Bottom Ad [Post Page]

| Designed by Colorlib | Distributed By Best BlogSpot Templates