Full width home advertisement

Travel the world

Climb the mountains

Post Page Advertisement [Top]

Ana Kishin-Kishin Din Soyayya Mai Karfi A Tsakanin Adam Zango Da Fati Washa

A dan iskan nan mai kadawa maganganun dake ta yawo a bakunan jama'a dai yanzu shine irin so da kauna mai karfin gaske da a ke zargin ya shiga tsakanin fitattun jaruman nan na wasan Hausa fim a masana'antar Kannywood watau Adam Zango da Fati Washa.
Wannan dai na zuwa ne lokacin da hotunan jaruman biyu a tare cikin raha da daman gaske ke cigaba da bayyana a kafafen sada zumunta na zamani inda kasafai ake ganin su suna ta raha suna dariya.
Haka zalika mun Samu cewa masu sharhi akan al'amurran yau da kullum a masana'antar shiya fina-finan ta Kannywood sun lura da cewa yanzu fina-finan da jaruman biyu keyi a tare na ta kara yawa a kasuwanni.
Sai dai kuma duk da maganganun dake ta yawo a kan lamarin, har yanzu jaruman sun ki fito su tabbatar ko kuma su karyata batun wanda hakan ke kara darsa kokwanto a zukatan masu sha'awar fina-finan.

No comments:

Post a Comment

Bottom Ad [Post Page]

| Designed by Colorlib | Distributed By Best BlogSpot Templates