Shehu Sani yayi Allah-wadai da kin sa hannu a sabon kudirin tsarin zabe
LABARAI DAGA 24BLOG
Sanata Shehu Sani wanda ke wakiltar Yankin Jihar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawan kasar nan ya tofa albarkacin bakin sa game da kudirin sauya dokar tsarin zabe da Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma yin watsi da shi.
Sanatan na Jam’iyyar PRP yayi tir da matakin da Shugaban kasar ya dauka na kin sa hannu a kan sabon kudirin tsarin zaben da Majalisar Tarayya ta aiko masa. Shugaban kasa Buhari yayi watsi da kudirin ne a Ranar Juma’ar nan.
Sani ya bayyana cewa cin amanar tsarin Damukaradiyya ne a ce Buhari yayi fatali da wannan kudiri da zai gyara harkar zaben kasar. Sanatan ya ba Shugaban kasar shawara ya guji biyewa wadanda ke kokarin murde zaben 2019.S
Sanatan yayi wannan jawabi ne a shafin sa na sadarwa na Tuwita bayan Shugaba Buhari ya maidawa Majalisa kudirin zaben a wani karo. Kwamared Shehu Sani yace akwai masu gudun ayi zaben ke-ke-da-ke-ke a Gwamnatin APC.
‘Dan Majalisar yayi mamakin yadda Gwamnatin nan ke gudun ayi zaben adalci a badi, ganin cewa irin wannan zabe na kwarai ne ya jawo APC tayi nasara. Sanatan ya kuma koka da yadda ake muzgunuwa ‘Yan adawa a halin yanzu.
No comments:
Post a Comment