[post by samaila umar lameedo]
Na zama 'Baba go slow' saboda dimokuradiyya – Buhari
LABARAI DAGA 24BLOG.NET
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce mutane suna kiran shi da sunan 'Baba go slow" ne saboda yana yaki da rashawa bisa tsarin da mulkin dimokuradiya ya shimfida.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da wasu mazauna Abuja suka kai masa gaisuwar barka da Kirsimeti karkashin jagorancin ministan Abuja a ranar Talata.
Buhari ya ce ya yi watsi da bin tsarin mulkin soja don yaki da rashawa.
Me Buhari ya ce game da kashe-kashen Zamfara?
An sanya dokar hana fita a Tsafe ta Zamfara
"Lokacin da ina sauri an cafke ni, yanzu don me zan yi sauri." in ji shi.
Ya ce tsarin ne ya zo da haka ba Baba ba, "duk da haka ba zan dakatar da farautar wadanda suka saci amanar kudaden al'umma ba da aka damka ma su."
Alkiblar yakin neman zaben Buhari
A yayin da yake shirin kaddamar da yakin neman zabensa a 2019, shugaban ya yaddada manyan abubuwan da gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali akai.
Ya ce yakin neman zabensa zai karkata ne ga nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fannin tsaro da tattalin arziki da yaki da rashawa.
"Za mu tafi yankunan Najeriya domin tunatar da su alkawullan da muka dauka a 2015 musamman fannoni uku, tsaro da tattalin arziki da yaki da rashawa." in ji shi.
Ya ce mutanen yankin arewa maso gabashi sun tabbatar da nasarar da aka samu a yaki da Boko Haram.
Buhari ya tura babban hafsan sojin sama zuwa Zamfara da Sokoto
Hotunan kaddamar da yakin neman zaben Atiku Abubakar
Sai dai kuma game da batun 'yan bindiga da barayin shanu da masu garkuwa da mutane da ke addabar jihohin yankin arewa maso yamma, shugaban ya ce gwamnatinsa a shirye take ta kawo karshen matsalolin.
A ranar Litinin al'ummar Zamfara suka gudanar da zanga-zangar nuna damuwa da yawan kashe-kashen mutane da ake yi a jihar.
Duk da sojoji da 'yan sanda da aka tura a Zamfara, amma har yanzu al'ummar jihar na cewa babu wani sauki ga matsalar tsaron da suke fuskanta.
A shafe shekaru ana ci gaba da samun matsalolin satar mutane don kudin fansa da hare-haren 'yan bindiga a sassan jihar Zamfara.
No comments:
Post a Comment