[post by samaila umar lameedo]
'Ba za mu daina fitowa ba har sai an saki Elzakzaky'
LABARAI DAGA 24BLOG
Mabiya mazhabar Shi'a karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Elzakzaky sun ce idan har ba a saki shugaban nasu ba to fa ba za su daina jerin gwano a kan titunan Najeriya ba.
A jiya Juma'a 'yan kungiyar ta IMN suka yi wani jerin gwano daga babban masallacin juma'ar Abuja inda suka kewaya babban birnin.
Sheikh Abdurrahman Yola wanda daya ne daga cikin jagororin zanga-zangar ta neman a saki Elzakzaky, ya shaida wa BBC cewa "Shekaru biyu ke nan da wata babbar kotu a Abuja ta bayar da iznin sakin shugaban nasu amma gwamnati ta yi burus", inda ya ce sakin shugaban nasu ne kawai mafita.
A watan Disambar 2015 ne dai jami'an tsaron Najeriya suka kama Ibrahim Elzakzaky bayan far wa gidansa bisa zargin tare wa hafsan sojojin kasan kasar hanya a Zariya.
Mabiya mazhabar sun sha musanta zargin sojojin inda suka ce zargin tare hanyar togaciya ce ta kai musu hari.
An yi zanga-zanga kan kwana 1000 da tsare el-Zakzaky
Ba za mu manta da gwamnatin Buhari ba — Shi'a
Tun dai wannan lokacin ne 'yan kungiyar ta IMN suke ta hawa tituna suna zanga-zangar kiran a saki shugaban nasu da matarsa da sauran 'yan kungiyar da ke tsare.
A 'yan watannin da suka gabata ne wata kotu a Kaduna ta saki wasu daga cikin 'yan kunggiyar fiye da 80.
No comments:
Post a Comment