[post by samaila umar lameedo]
Babu sunan Tambuwal a cikin 'yan takarar gwamnan Sokoto
LABARAI DAGA 24BLOG
Hukumar zaben Najeriya reshen jihar Sokoto ta ce babu sunan gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal a jerin sunayen wadanda suka cancanci tsayawa a zaben 2019.
Kwamishinan hukumar zaben jihar, Malam Sadik Abubakar Musa, ya shaida wa BBC cewa jam'iyyar PDP mai hamayya, ta mika sunan Alhaji Mannir Dan Iya ne a matsayin dan takararta na mukamin gwamnan.
Wannan dai ya saba wa tunanin mutane da dama a jihar cewa Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ne jam'iyyarsa ta PDP za ta tsayar takarar gwamna bayan da ya kasa samun tikitin takarar shugabancin kasar a watan Satumba.
Tambuwal zai tsaya takarar shugaban kasa
Abin da ya sa na koma PDP - Tambuwal
Da ma dai Alhaji Dan Iyan ne ya samu tikitin takarar gwamnan babu hamayya a zaben fitar da gwani na ranar a watan Satumba, amma sai wasu majiyoyin jam'iyyar suka ce ya amince ya janye wa gwamnan jihar bayan da ya fadi a zaben fitar da gwani na shugaban kasa.
Sai dai jami'in hukumar zaben ya ce jam'iyyar na da har nan da ranar daya ga watan Disamba ta sauya sunan dan takarar idan tana bukatar yin hakan.
"Jam'iyyun suna da lokaci wanda za su iya canza sunan 'yan takara ko kuma dan takara ya ce ya janye. Daga nan har ranar 1 ga watan Disamba za su iya yin hakan," in ji shi.
No comments:
Post a Comment