An kashe fiye da Musulmi 40 a taron Maulidi
LABARAI DAGA 24BLOG
An kashe akalla mutum 43 a wani harin kunar bakin wake da aka kai a dakin taron da ake gudanar da taron Maulidi a Kabul, babban birnin Afghanistan.
Jami'ai sun ce akalla mutum 83 ne suka jikkata lokacin da malaman addinin Musulunci suke taro a babban dakin da ke lardin PD15 domin tunawa da zagayowar ranar haihuwar annabi Muhammad (SAW).
Harin shi ne mafi muni da aka kai Kabul a watannin baya bayan nan.
Babu wanda ya dauki nauyin kai harin, sai dai kungiyar IS ta sha daukar alhakin hare-haren da aka kai a birnin a baya bayan nan.
Hare-haren da kungiyar Taliban ke yawan kai wa sun sa an kara tsaurara matakan tsaro.
Da gaske ne Shehu Ibrahim Nyass ya bayyana a Maulidin Abuja?
Hotunan bikin Maulidin Shiekh Ibrahim Nyass a Abuja
Akalla mutum 1,000 ne a dakin taron lokacin da aka kai harin, in ji jaridar Tolo.
1TV News ta ambato jami'an kula da lafiya na cewa mutum 24 sun ji mummunan rauni.
Wani manajan da ke kula da dakin taron ya ce dan kunar bakin aken ya tashi bam din da ke jikinsa a tsakiyar masu bikin Maulidin
Kungiyar IS ta ce ita ce ta kai hari biyu a Kabul a watan Agusta wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Kazalika ita ta kai harin da ya halaka mutane da dama da ke kada kuri'a lokacin zaben majalisar dokokin kasar a watan Oktoba.
Sai dai a kwanakin baya bayan nan an rika yunkurin sulhu domin kawo karshen irin wadannan hare-hare da aka kwashe shekara da shekaru ana kai wa kasar.
No comments:
Post a Comment