Almundahana: Kotu ta ki amincewa da bukatar EFCC a kan Shekarau
LABARAI DAGA 24BLOG
- Kotu ta ki amince da bukatar Hukumar EFFC na mayar da Shari'ar tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau zuwa Abuja
- Hukumar EFCC tayi ikirarin cewa lauyoyinta da shedu na cikin fargaba sakamakon barazana ga rayuwansa da magoya bayan Shekarau ke musu a Kano
- Sai dai lauya mai kare Shekarau, Sam Ologunorisa ya ki amincewa da wannan bukatar da ya ce ta sabawa doka kuma da alamun EFCC ba ta shirya ba
Babban Kotun Gwamnatin Tarayya da ke Kano ta ki amincewa da bukatar da hukumar yaki da rashawa (EFCC) ta nema na mayar da shari'ar zargin almundaha da ake yiwa tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekaru zuwa Abuja.
Mai shari'a Lius Allagoa ya yi watsi da bukatar na EFCC bayan ya saurari hujoji daga bangarorin masu shigar da kara da mai kare wanda ke zargi.
Lauyoyin EFCC sun nemi a mayar da shari'ar zuwa Abuja ne saboda dalilin rashin tsaro.
Almundahana: Kotu ta ki amincewa da bukatar EFCC a kan Shekarau
A yayin shigar da karar, lauyan EFCC Johnson Ojojbane ya ce suna nema a mayar da shari'ar zuwa Abuja ne saboda abinda ya kira tabarbarewar tsaro sakamakon rikicin da akayi tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan Shekarau a ranar da aka fara gurfanar da shi a kotu.
DUBA WANNAN: Masifar da ta fi Boko Haram na nan tafe a kasar nan - Sarki Sanusi
Ya ce kiris ya rage da magoya bayan Shekarau sun yiwa abokan aikinsa da shi kansa rauni kafin yan sanda su kawo musu taimako.
"Sakamakon tashin hankalin da muka fuskanta a ranar da aka fara shari'ar da kuma barzanar da aka cigaba da yi mana, muna cikin fargaba.
"Shedun mu guda uku suma suna tsoron su bayyana a gaban kotu su bayar da sheda saboada barazanar da wasu mutane da bamu gano ko su wanene ba ke musu.
"A halin yanzu mutum daya ne kawai daga cikinsu ya amince a ambacci sunansa cikin takardar rantsuwar da za a gabatar a kotu," inji Ojojbane
EFCC tana tuhumar Shekarau ne tare da tsohon Ministan Harkokin Kasashen Waje, Aminu Wali da wani Mansur Ahmad da aikata laifuka guda shida masu alaka da karkatar da kudi wanda adadinsu ya ka N950 miliyan.
A bangarensa lauya mai kare shekarau, Mr Sam Ologunorisa ya yi ikirarin cewa lauyoyin EFCC ba su shirya da cigaba da shari'ar bane kuma bukatar su ta canja wajen shari'ar ya sabawa doka.
Allagoa ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 4 ga watan Disamban 2018.
No comments:
Post a Comment