Full width home advertisement

Travel the world

Climb the mountains

Post Page Advertisement [Top]


Wani hedimasta na makarantar firamare ta Alhazawa dake karamar hukumar Danja a jihar Katsina, mai suna Kabiru Husaini yana ci gaba da zama a gidan kaso biyo bayan zarginsa da yi wa yarinya daliba 'yar shekara goma fyade.
Hedimastan, wanda mazaunin Sabon Gari ne dake garin Zaria, rahotanni sun nuna cewa ya jima yana amfani da yarinyar a cikin ajujuwan makarantar.
Mahaifin yarinyar, shi ya gano hakan a ranar 26 ga watan Janairu, 2020.
Hedimastan dai zai ci gaba da zama a gidan kaso har zuwa ranar 14 ga watan Afrilu, 2020 kafin gurfanar da shi a gaban kotun majestiri karkashin jagorancin Hajiya Fadile Dikko.

No comments:

Post a Comment

Bottom Ad [Post Page]

| Designed by Colorlib | Distributed By Best BlogSpot Templates